Theresa May da mijinta Philip John May sun isa fadar firaministan kasar tare da yin jawabi. A cikin jawabinta, May ta yi alkawarin kawar da rashin adalci a zamantakewar al'ummar kasar, da kuma tinkarar kalubale bayan da kasar ta janye daga kungiyar EU.
Bayan da Theresa May ta shiga fadar firaministan kasar, ta nada sabbin ministocin gwamnatin kasar nan da nan. An nada tsohon ministan harkokin wajen kasar Philip Hammond a matsayin ministan kudi, tsohon magajin birnin London kuma babban jagora kan janyewar Birtaniya daga EU Boris Johnson ya zama ministan harkokin wajen kasar, tsohon ministan kula da makamashi da sauyin yanayi na kasar Amber Rudd a matsayin ministan harkokin cikin gida, kuma ministan tsaron kasar Michael Fallon ya ci gaba da zama mukaminsa.
Hakazalika kuma, Theresa May ta nada Davies David a matsayin ministan kula da harkokin kasar na janyewa daga EU, wannan mukami sabo ne da aka kafa a wannan karo. (Zainab)