Ministan lafiya na Jamhuriyar demokiradiyar Congo Felix Kabange ya bayyana cewa, hukumar lafiya ta duniya WHO ta aikawa kasarsa sama da alluran cutar shawara miliyan 11, baya ga allurai miliyan 12.5 da mahukunatn kasar suka yi oda daga kasashen Sin da Indiya.
Ministan ya kuma tabbatar da cewa, an samu barkewar cutar ta shawara a larduna uku na kasar.
Ya ce, za a kaddamar da kamfel din ilimantar da jama'a game da illolin cutar a watan Yulin, inda za a shafe kwanaki 10 zuwa 12 ana gudanarwa.(Ibrahim)