in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta damke mutane 134,000 dake da hannu a ta'ammali da miyagun kwayoyi
2016-06-26 17:47:40 cri
Hukumar dake sa ido kan amfani da kwayoyi dake sa maye ta kasar Sin NNCC, ta sanar a yau Lahadi cewa, jami'an 'yan sandan kasar sun kama mutane 134,000 wadanda take zarginsu da hannu wajen aikata laifuka kimanin 113,000 da suka shafi ta'ammali da haramtattun kwayoyi cikin shekarar data gabata.

Mamba a majalisar gudanarwa ta kasar Sin kana shugaban hukumar ta NNCC Guo Shengkun, ya ziyarci cibiyar dake kula da masu ta'ammali da kwayoyi masu sa maye wadda ke karkashin ikon hukumar tsaron jama'a ta birnin Beijing, tun a ranar Juma'ar da ta gabata gabannin bikin tunawa da ranar yaki da safarar haramtattun kwayoyi ta MDD wanda ake gudanarwa a duk ranar 26 ga watan Yunin kowace shekara.

Guo, ya bukaci a cigaba da yaki da wannan muguwar dabi'a ta ta'ammali da haramtattun kwayoyi, yana mai cewa za'a dauki dukkan matakan da suka dace domin kawar da wannan muguwar dabi'a a tsakanin alumma.

Jami'in ya jaddada muhimmancin daukar tsauraran matakai kan dukkan wadanda aka kama da hannu wajen aikata laifukan ta'ammali da miyagun kwayoyi domin ya zama darasi ga masu sha'awar aikata laifukan.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China