A yayin ganawar wadda ta gudana a hedkwatar kungiyar AU da ke birnin Addis Ababa na kasar Habasha daga ranar 7 zuwa 8 ga wata, tawagar ta tattauna batutuwan da suka shafi shata taswirar da za ta kai ga kaddamar da wannan hukuma.
A cikin watan Afrilun shekarar 2014 ne ministocin kiwon lafiya na kasashen Afirka suka amince a kafa hukumar kula da magunguna ta Afirka,wadda za a dora mata alhakin sanya ido kan irin kayayyakin kiwon lafiya da suke wadari a kasuwannin Afirka.
Bugu da kari, ana sa ran hukumar ta kasance babbar mai sanya ido wajen magance kayayyakin lafiya na jabu, baiwa magungunan da ake sarrafa a cikin gida damar yin takara, musamman magungunan cututtukan da ke damun kasashen Afirka.(Ibrahim)




