
Jakadan Sin a kasar Zhao Yanbo ya karbi lambar yabon a madadin shugaba Xi na kasar Sin. Mataimakin shugaban kasar da raguwar majalisar ministocin kasar da sauran jami'an diplomasiyya na kasashen waje da ke kasar sama da 100 sun halarci wannan biki.
A lokacin da ya ke mika lambar yabon, shugaban Koroma ya bayyana cewa, gwamnatin Sin karkashin shugabancin Xi Jinping, ta ba da gudummawa da agajin jin kai ga kasar Saliyo, lamarin da ya ingiza bunkasuwar kasar, musamman ma aniyar shugaban Xi ta ba da agaji da fasahohi cikin lokaci ga kasar Saliyo wajen tinkarar cutar Ebola, abun da ya nuna hadin gwiwar kasashen biyu.
Shugaban Koroma ya tsaida kudurin karrama shugaba Xi Jinping da babbar lambar yabon ne domin nuna godiya ga kasar Sin. A madadin shugaba Xi, jakadan Zhao ya karbi lambar yabon da takardar shaida, daga bisani ya mika godiyar shugaba Xi ga shugaba Koroma.(Bako)




