in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta duniya
2016-05-05 10:17:01 cri

A ranar Litinin 25 ga watan Afrilun shekarar 2016 ne aka yi bikin ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta duniya na wannan shekara.

Majalisar dinkin duniya ce ta kebe wannan rana a duk shekara domin ganin an kawar da cutar daga doron duniyarmu.

Alkaluma na nuna cewa mutane 438,000 ne ke mutuwa a duk shekara sanadiyyar wannan cutar, kana mutane miliyan 214 na kamuwa da cutar, kuma kashi 90 cikin 100 na wadanda ke kamuwa da cutar ta malaria a nahiyar Afirka suke.

Masana harkar lafiya sun kuma bayyana cewa, muddin ba a dauki matakan da suka dace ba mutane da dama na fuskantar barazanar kamuwa da cutar a duniya.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyawa cewa, tun a shekarar da ta gabata ce kasashen Turai suka yi nasarar cimma burin kawar da cutar zazzabin cizon sauro..

Amma duk da irin wannan nasara da kasashen Turai suka cimma har yanzu cutar zazzabin cizon sauro na mummunar barna a kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta ce akwai kyakkyawan fatan kawar da cutar zazzabin cizon sauro a duniya baki daya, karkashin shirin da aka tsara a takardar fasahohin ba da jinya da rigakafin ciwon tun daga bana zuwa shekarar 2030 mai zuwa.

Kaza lika, bisa rahoton zazzabin cizon sauron na duniya na bara wanda hukumar WHO ta fitar, an ce an samu babbar raguwa kan adadin masu kamu da ciwon, musamman mutanen da ke rasuwa sakamakon ciwon tun daga shekara ta 2000, sai dai a daya hannun, an cimma wannan nasara ne ta hanyoyin yin amfani da gidan sauro, da bincike, da kuma samar da magungunan cutar ta zazzabin sauro da dai sauran su.

Sai dai ya zuwa yanzu, ana ci gaba da fuskantar babban kalubale kan wannan aiki, sabo da kusan rabin mutanen duniya suna fuskantar kalubalen kamuwa da wannan cuta, inda a shekarar 2015, aka samu karin mutane miliyan 214 da suka kamu da cutar, yayin da dubu 438 suka rasu sakamakon kamuwa da cutar, kuma galibin su daga kudancin Sahara..

Kaza lika, a halin yanzu mutane sama da miliyan ba su iya samun kulawa yadda ya kamata, wajen kare kan su daga wannan cuta. An dai kebe ranar 25 ga watan Afrilun ko wace shekara, a matsayin ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta duniya. Taken bikin na bana shi ne, "kawo karshen yaduwar zazzabin cizon sauro a duniya".

Masana na cewa, wajibi ne al'umma ta tashi tsaye wajen tsaftace muhalli, tare da tallafawa kokarin mahukunta da sauran kungiyoyi na gida da na waje na ganin an yaki da wannan cuta da ke halaka yara da mata masu juna biyu baki daya. (Ibrahim/Saminu/Maman/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China