A jiya ranar 30 ga watan Afrilu, shugabar kasar Liberia Ellen Johnson-Sirleaf ta gana da rundunar 'yan sandan kiyaye zaman lafiya ta hudu dake kasar Liberia a birnin Monrovia, inda ta yabawa aikin rundunar game da gudummawar da ta samar sosai wajen tabbatar da zaman lafiya da samun bunkasuwa a kasar Liberia.
A yayin ganawar, madam Sirleaf ta bayyana cewa, jama'ar kasar Sin abokan jama'ar kasar Liberia ne, tare da nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin game da goyon baya da taimako da take kawowa ga kasar wajen kiyaye zaman lafiya da samun bunkasuwa. Jama'ar kasar Liberia suna maraba da zuwan rundunar 'yan sandan kiyaye zaman lafiya na kasar Sin, da nuna godiya gare su bisa kokarin da suke yi na gudanar da ayyukansu. (Zainab)