Najeriya ta gaza samun gurbin shiga gasar volleyball wadda za a yi a yayin wasannin Olympics na Rio
Kungiyar 'yan wasa mata ta Najeriya, ta gaza samun gurbin shiga gasar kwallon raga ta volleyball da ake yi kan rairayi, wadda kasashen duniya za su shiga a gasar Olympics ta birnin Rio nan gaba cikin wannan shekara.
Najeriya dai ta karbi bakuncin kasashe 9 a wasan share fagen gasar ta Rio da aka gudanar, a bakin ruwa dake yankin Jabin jihar Legas, sai dai ta yi rashin nasara a hannun kasar Masar, a wasan kusa da na karshe na cin kofin CAVB, wanda ke matsayin gasar share fagen gasar ta Olympic.(Saminu Alhassan)