in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zhang Gaoli ya halarci taron koli kan bunkasuwar kasar Sin
2016-03-20 19:09:19 cri
A yau Lahadi ne aka bude taron koli na shekara-shekara game da saamr da bunkasuwar kasar Sin.

Zaunannen mamba na hukumar siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma mataimakin firaministan kasar Zhang Gaoli ya halarci bikin tare da yin jawabi.

Zhang ya ce, yayin da aka zurfafa dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya, don samun moriya ga daukacin kasashen duniyar, kasar Sin ta ci moriyar dunkulewar tattalin arzikin na duniya, kuma ta bada babbar gudummawa game da samar da zaman lafiya a sha'anin tattalin arzikin duniya.

Bunkasuwar da Sin ta samu, zai bada damar hadin gwiwa da fadada harkokin kasuwanci da zuba jari a kasuwannin duniya, ta yadda kasar zata ci gajiya dama sauran kasashen duniya baki daya.

Cibiyar nazarin raya kasa ta majalisar gudanarwar kasar Sin ce ta shirya taron tattaunawar na wannan karo, kuma taken taron na wannan karon shi ne, tsara shirin raya kasa cikin shekaru biyar masu zuwa, kwararru da masana da masu masaana'antu da jami'an gwamnatocin kasashen duniya, kana da wakilan hukumomin kasa da kasa sun halarci bikin bude wannan taro.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China