in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin watsa labaran ketare suna mai da hankali kan rufe taruka biyu na Sin
2016-03-17 10:25:01 cri

A jiya Laraba da safe ne, aka kammala zaman taro na hudu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC na 12 a babban dakin taron jama'ar kasar Sin dake birnin Beijing, inda kafofin watsa labarai na ketare suka mai da hankali kan yadda aka zartas da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 13 da kuma kyakkyawan fata da imani da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya nuna kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a yayin taron maneman labarai da aka yi a jiya.

Kamfanin dillancin labarai na Faransa watau AFP ya ba da rahoto cewa, an zartas da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 13 na kasar Sin da kuma dokar jin kai a yayin zaman taro na hudu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC na 12. Haka kuma, bisa shirin din da aka tsara, ya zuwa shekarar 2020, ma'aunin tattalin arziki na GDP na kasar Sin zai karu daga kudin Sin RMB biliyan 67700 na shekarar 2015 zuwa RMB biliyan 92700.

Bugu da kari, kamfanin dillancin labarai na Associated Press na kasar Amurka ya fidda rahoton cewa, shugabannin kasar Sin sun sha jaddada muhimmancin kiyaye ci gaban tattalin arziki a kasar, haka kuma, ana sa ran farfadowar kasuwannin kasar sakamakon wasu matakai da gwamnatin kasar Sin ta bullo da su. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China