in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawarwarin da aka gabatar a manyan tarukan Sin na shekara 2016
2016-03-17 08:09:01 cri

Tun lokacin da aka kaddamar da manyan tarukan kasar Sin na shekara-shekara wato taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC da taron wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC na shekarar 2016 a nan birnin Beijing, wakilai da mambobi na majalisun suke bayar da shawarwari kan yadda za a aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 13.

Rahotanni na nuna cewa, ya zuwa karfe 5 na yammacin ranar 8 ga watan Maris na shekarar 2016, an gabatar da shirye-shirye 5375 a gaban majalisar, kuma an yanke shawarar tattaunawa kan shirye-shirye 4248. Shawarwarin da suka fi daukar hankali sun hada da kokarin kyautata tsarin samar da kayayyaki ta hanyar yin kwaskwarima, aiwatar da tsare-tsaren raya kasa ta hanyar yin kirkire-kirkire, kara bude kofa ga kasashen waje, kyautata tsarin bada rangwame a fannin kiyaye muhalli, cusawa jama'a akidar kiyaye tsaron kasa da dai sauransu.

Bugu da kari, sauran fannonin da aka tabo sun hada da sabbin manufofin diflomasiya na kasar Sin da manyan kasashen duniya, raya birane da kauyuka, tsarin mallakar filayen itatuwa da batun kula da tsofaffi, matakin da masana suka ce zai kara karfafawa matasa gwiwa su ba da tasu gudummawa ga ci gaban kasa.

Haka zalika, wakilan jama'a da mambobi na majalisun sun tattauna kan batun kare 'yancin mallakar fasaha, yaki da cin hanci da rashawa, inda gwamnatin kasar Sin ta ce za ta kara tsaurara matakan magance wannan matsala. Sauran batutuwan sun hada da sakawa wadanda suka nuna kwazo, gaskiya da rikon amana a ayyukansu da sauransu.

Masu fashin baki na cewa, shawarwarin da aka gabatar a wadannan taruka, za su taka muhimmiyar rawa ga alkiblar kasar Sin a yayin da take shirin aiwatar da shirinta na raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 13. (Ibrahim/Ahmad/Saminu/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China