in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Uganda zai fuskanci shari'a game da sakamakon zaben kasar
2016-03-03 10:36:05 cri

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni zai fuskanci tuhuma yayin da 'yan adawar kasar suka garzaya kotu domin kalubalantar sakamakon zaben kasar na ranar 18 ga watan Fabrairu, wanda aka ayyana shugaban mai ci a matsayin mutumin da ya lashe zaben.

Jam'iyyar adawa ta FDC wanda Kizza Besigye ya tsayawa takara ita ce ta zo ta biyu a bisa sakamakon zaben, jam'iyyar ta sheda wa 'yan jaridu cewar, akwai tuhuma game da sahihancin sakamakon zaben, kuma suna zargin an tafka magudi.

Sanarwar ta ce, ci gaba da yin kawanya da jami'an tsaron kasar ke yi a gidan Besigye, da kuma yawan kamen da jami'an 'yan sanda ke yi na 'yan adawa ya dakile aniyar jam'iyyar ta kalubalantar zaben a gaban babbar kotun shari'ar kasar.

Amma Mbabazi, guda ne daga cikin 'yan takarar shugabancin kasar, tuni ya kalubalanci sakamakon zaben a gaban babbar kotun shari'a ta kasar.

Shi dai Mbabazi, yana zargin shugaba Museveni da magoya bayansa da laifin keta dokokin zabe, daga cikin laifukan har da zargin raba kudaden ga masu kada kuri'a, da tada husuma a lokacin zaben, da yin kalaman batanci, da tsare abokan hamayya ba bisa ka'ida ba, da kuma kamawa tare da kulle magoya bayan jam'iyyun adawar kasar, har ma da tarwatsa su, a cewar 'yan adawar, dukkan wadannan laifuka sun saba dokokin hukumar zaben kasar. Mbabazi ya bukaci kotun da ta gaggauta soke zaben.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China