in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar shugaban Najeriya a kasashen Saudiya da Qatar
2016-02-25 13:51:51 cri

A ranar Litinin 22 ga watan Fabrairun shekarar 2016 ne shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya fara ziyarar aiki ta tsawon mako guda a kasashen Saudiyya da Qatar domin tattaunawa game da hanyoyin kyautata farashin danyen mai wanda ke ci gaba da faduwa a kasuwannin duniya.

Wata sanarwar da fadar shugaban kasar Najeriya ta fitar ta nuna cewa, zangon farko ta ziyarar shugaba Buhari, ita ce birnin Riyadh, fadar mulkin kasar Saudiya inda ya tattauna da sarki Salman Bin Abdulaziz Al Saud da manyan jami'an kasar ta Saudiyya.

Bugu da kari, shugaba Buhari ya gana da sarki Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani na Qatar duk da nufin tattauna batun farashin man fetur.

Ana sa ran wannan yunkuri na mahukuntan Najeriya da sauran kasashe mambobin kungiyar dake fitar da danyen mai a duniya wato OPEC, za ta samar da kyakkyawar alkibla game da daidaituwar farashin danyen man dake ci gaba da karyewa.

Bayanai na nuna cewa, ana kuma sa ran shugaba Buhari zai gana da 'yan kasuwa a wadannan kasashe biyu ta yadda za su taimaka wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya, ta hanyar zuba jari a fannonin hako ma'adinai, aikin gona, makamashi, sufuri, sadarwa, kayayyakin more rayuwa da sauransu.

Masu fashin baki na cewa, kasar Saudiya tana da rawar da za ta taka dangane da kyautata farashin mai da ke ci gaba da faduwa a kasuwannin duniya, duk da adawar da wasu mambobin kungiyar OPEC ke yi game da matakan da Saudiya da Rasha da sauransu ke kokarin dauka na kyautata farashin mai.

Najeriya dai ta dogara ne da mai wajen samun kudaden shigarta, kuma wannan mataki da shugaba Buhari ya dauka a cewar masana, zai taimaka wajen inganta tattalin arzikin kasar da ya durkushe tare da janyo masu sha'awar zuba jari cikin kasar, ta yadda za su ba da tasu gudummawa a kokarin da mahukuntan kasar ke yi na ganin tagomashin kasar ya dawo a idon duniya.

Masu fashin baki na ganin cewa, kamata ya yi kasashen duniya su lalubu wasu hanyoyin samun kudaden shiga kamar ma'adinai da wasu kafofin maimakon dogara kwacakwam kan man fetur. (Ibrahim, Saminu Alhassan, Ahmad Fagam, Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China