Dan wasan mai shekaru 23 an yi amanna cewar, zai iya yarda sauya shekarsa zuwa tsarin wasannin Premier League na kasar Birtaniya.
Sai dai kuma, CSKA, wanda shi ne babban kulob din wasannin Premier ta kasar Rasha yana so a jinkirta wannan yunkurin har zuwa lokacin zafin bana.
Musa ya sake daukar hankalin manyan kuloflikan tsarin gasar Premier League na Birtaniya ,wanda aka kayyade cikin kwantiragin zuwa shekarar 2019 cewa, ba za a sami dan wasan ba kafin an biya dala miliyan 32 da rabi ba.(Ahmad Fagam)