Wata sanarwar da babban sakataren kungiyar ta IGAD Mahboub Maalim ya fitar a birnin Nairobin kasar Kenya, ta bayyana amincewarsa da manufofin yaki da tsattsauran ra'ayi, wadanda babban magatakardar MDD ya gabatar a kwanakin baya, matakin da ke da nufin kandagarki, tare da fuskantar kalubalen da 'yan ta'adda ke haifarwa ga rayuwar bil'Adama.
Sanarwar ta kuma bayyana bukatar dake akwai, ta hada karfi da karfe da daukacin kasashen duniya, wajen dakile dalilan da ke haifar da yaduwar tsattsauran ra'ayi, kamar yadda hakan ke kunshe cikin tsarin zartaswa na MDD.
Maalim ya jaddada cewa, zartas da manufofin dake kunshe cikin tsarin na MDD, na bukatar hadin kai daga sassan masu ruwa da tsaki a mataki na shiyya-shiyya da kuma na kasa da kasa.