Wani babban jami'in asibitin gundumar wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana wa manema labarai cewa, an kawo gawawwakin mutane a kalla 19 da harin ya rutsa da su.
Shi ma ministan kula da lafiyar jama'a na lardin Khyber Pakhtunkhwa, Shah Farman, ya tabbatar da jikkatar sama da mutane 50.
Kakakin sojojin Pakistan Asim Saleem Bajwa ya tabbatar a shafinsa na sada zumunta na twitter cewa, jami'an tsaro sun yi nasarar kashe a kalla 'yan bindiga 4 . Ana kuma gudanar da bincike don kamo sauran 'yan bindigan da suka gudu.
Kafofin watsa labarai sun bayyana cewa,an yi nasarar kwashe dukkan dalibai da ma'aikatan jami'ar ba tare da samun ko kwarzane ba.
A wani labarin kuma, shugaban kasar Maldives Adulla Yameen ya yi allah wadai da harin ta'addancin da aka kai jami'ar ta Pakistan
Ya kuma bayyana goyon bayan gwamnati da al'ummar Maldives a kokarin da mahukuntan Pakistan ke yi na yaki da ayyukan ta'addanci.
Har yanzu dai babu wani rahoto game da ko maharan sun yi garkuwa da wasu mutane. (Ibrahim)