A bana Luis Enrique ya samu nasara kan abokan takarar sa Josep Guardiola da kuma Jorge Sampaoli.
Luis Enrique dan shekaru 45 da haihuwa, ya jagoranci kungiyar Barcelona inda ta dauki kofuna uku a kakar wasa daya, nasarar da ita ce makamanciyar ta ta biyu a tarihin kafuwar kungiyar.
A shekarar 2015 kofin Spanish Super Cup ne kadai Enrique bai samu damar dauka ba, amma duk da hakan ana yiwa kungiyar ta Barcelona da yake horaswa, kallon zakaran gwajin dafi a tsakanin kulaflikan Sifaniya, da ma na sauran sassan duniya baki daya.
Enrique tare da tallafin manyan 'yan wasan Barcelona kamar su Lionel Messi, da Luis Suarez da Neymar, sun cimma nasarar lashe wasanni har guda 50 a shekarar ta 2015.(Saminu Alhassan)