Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya bayyana a ranar Laraba cewa, za a aiwatar da yarjejeniyar nukiliyan Iran a 'yan kwanaki masu zuwa. Ranar aiwatarwa, ita ce ranar da Iran za ta nuna niyyarta na janye shirinta baya, kana kar ma ta nemi wani sassauci na takunkunmi, za ta zo nan ba da jimawa ba, wata kila nan da 'yan kwanaki, in ji shugaban diplomasiyyar Amurka a cikin wani jawabin siyasar waje a jami'ar tsaron kasa.
Mista Kerry ya bayyana cewa, aiwatar da yarjejeniya kan batun nukiliyar Iran, da ya kimanta a matsayin wani tsarin na toshe duk wasu hanyoyin da za su baiwa Iran kai ga samun makamin nukiliya, zai kasancewa wani muhimmin aikin siyasar wajen Amurka a shekara mai zuwa.
Zan tabbatar muku cewa, za mu ci gaba da sanya ido yadda ya kamata kan aiwatar da wannan yarjejeniya, domin cewa gaskiya har yanzu muhimman kalubale ke cikin wannan batu, in ji John Kerry. (Maman Ada)