Kungiyar hada kan kasashen Larabawa ko AL a takaice ta zargi kasar Iran da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasashen.
Shugaban kungiyar Nabil al-Arabi ne ya sanar da hakar yayin taron ministocin harkokin wajen kungiyar da ya gudana a kasar Masar don tattauna takaddamar siyasar da ta kunno kai tsakanin Saudiya da kasar Iran.
Nabil al-Arabi ya bukaci dukkan kasashen Larabawa da su dauki matsayi guda kan wannan takaddama. Sannan ya yi kira ga kasar Iran da ta daina tsamo baki a harkokin cikin gidan kasashen.
Taron kungiyar kasashen Larabawan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar mummunan zaman tankiya da barazanar tsaro a yankin gabas ta tsakiya.
Yanzu haka dai dukkan kasashen Larabawa sun bayyana cikakkiyar goyon bayan su ga kasar Saudiya.(Ibrahim)