in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Halin da ake ciki a kasar Sham
2016-01-07 16:04:54 cri

A ranar Jumma'a 18 ga watan Disamban shekarar 2015 ne kwamitin sulhu na MDD ya zartar da wani kuduri game da yadda za a daidaita batun kasar Syria ta hanyar siyasa. Kana a farkon watan Janairun shekarar 2016 ne ake fatan kammala aikin yin shawarwari tare da kungiyoyin adawa na kasar ta Syria, daga bisani kuma a kira taron shimfida zaman lafiya a ranar 25 ga watan na Janairu a birnin Geneva.

A baya kasashen Rasha da Amurka da kuma kawayenta a gyefe guda sun kasa warware bambance-bambancn dake tsakaninsu game da batun kasar ta Syria, musamman ma makomar shugaba Bashar al-Assad.

Ita dai Rasha tun ba yau ba ta bayyana cewa, tana kai hare-hare a Syria ne domin yaki da 'yan ta'adda tare da kawo daidaito a halaltacciyar gwamnatin Bashar al-Assad, matakain da Rasha ta ce zai taimaka wajen samar da yanayin da ya dace ga 'yan siyasar kasar Syria ta yadda za su yi ba-ni-gishiri-in-ba-ka manda.

Da farko kasashen yammacin duniya dai karkashin jagorancin Amurka na adawa da matakan soja da Rasha ke dauka a Syria. Sannan daga bisani ma'aikatar tsaron Amurka ta bayyana cewa, sojojinta za su dakatar da shirinsu na horas da kungiyar 'yan adawar kasar Sham, inda za a maye gurbin shirin ta hanyar tallafa musu da makamai domin yakar mayakan kungiyar IS.

Masana a harkar tsaro na ganin cewa, da alamun an dauko hanyar warware batun kasar Syria, ganin yadda yanzu manyan kasashen da a baya kansu ke rabe suka fara fahimtar juna, duk da cewa, ba rasa wasu 'yan bambance-bambancen da ke tsakaninsu ba.

Masu fashin baki na cewa, matakin da MDD ta dauko a wannan karo da kuma abubuwa da ke faruwa a zahiri daga bangarorin da lamarain ya shafa, ana fatan haka za ta cimma ruwa, kana daga karshe za a kawo karshen yadda ake salwantar da rayukan fararen hula a kasar ta Syria. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China