in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bullo da sabuwar dokar yaki da ta'addanci
2016-01-04 19:20:10 cri

A ranar Lahadi 27 ga wata Disamban shekarar 2015 ne hukumar tsara dokoki ta kasar Sin, wato zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya zartas da sabuwar dokar yaki da ta'addanci, dokar da za ta fara aiki a ranar 1 ga watan Janairu na shekarar 2016.

Wannan ita ce da ta farko da kasar Sin ta kafa a baya-bayan nan na yaki da ta'addanci a fadin kasar da kuma taimakawa wajen samar da tsaro a duniya baki daya.

Bisa tsarin sabuwar dokar, yanzu sojojin 'yantar da jama'a na kasar Sin, za su iya shiga ayyukan yaki da ta'addanci a ketare. Sannan gwamnati tana da iznin kwace kudaden duk wata kungiya da ake zargin tana taimakawa ayyukan ta'addanci na dan wani lokaci, haka kuma sabuwar dokar ba ta da nufin musgunawa wani addini ko kabila.

Sabuwar dokar ta tanadi kafa wata cibiyar binciken asiri ta kasa, wadda za ta rika aiki da sassa da hukumomin da abin ya shafa wajen tattara bayanai game da yaki da ayyukan ta'addanci.

Har ila, dokar za ta bullo da matakan karfafa yaki da ta'addanci, hana aukuwar ta'addanci, daidaita matsalolin ta'addanci da kuma hukunta masu aikata ayyukan ta'addanci bisa doka da kuma uwa uba hada kai da kasashen duniya don murkushe ta'addanci.

A karshe, sabuwar dokar ta bukaci kamfanonin wayoyin sadarwa da su taimakawa hukumomin tsaro kamar 'yan sanda da muhimman bayanan da za su kara taimakawa a yakin da ake yi da ayyukan ta'addanci a duniya.

Sai dai wasu na yi wa wannan doka wata fassara, matsayin wata dama ta keta 'yancin jama'a na fadin albarkacin baki. Amma manasa na ganin cewa, wannan muhimmin mataki ne a gwagwarmayr da ake na kakkabe bazanar ayyukan ta'addanci da ke addabar duniya a halin yanzu. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China