Carter ya bayyana wa kwamitin kula da aikin soja na majalisar wakilan Amurka a wannan rana cewa, bayan da aka cimma daidaito tare da gwamnatin kasar Iraki ne, sojojin kasar ta Amurka suka kafa rukunin sojojin na musamman, kuma ayyukansu sun hada da kai hari ba zato ba tsammani, kwato mutanen da aka yi garkuwa da su, leken asiri, kama shugabannin kungiyar IS.
Carter ya kara da cewa, sojojin na musamman za su kai harin ba zato ba tsammani bisa amincewar gwamnatin kasar Iraki, kuma manufar kai harin ita ce kara tabbatar da tsaron iyakar Iraki da kara karfin jami'an tsaron kasar Iraki. (Zainab)