in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hajiya Fatima Ibrahim Shema
2015-11-24 14:41:27 cri

Tun daga dawowar mulkin demokradiya a Nigeria,shugabanni a dukkan matakai suke karfafa ma matansu gwiwwa domin su kafa wassu cibiyoyi ko shirye-shirye da za su inganta rayuwar al'umma musamman mata, yara da kuma matasa.

To, galibin wadannan cibiyoyi ko kungiyoyi suna zaman kansu ne, wato ba na gwamnati ba ne, iyakacin dai za'a iya cewa ita gwamnatin ta san da zamansu. To daya daga cikin irin wadannan kungiyoyi ita ce Service to Humanity Foundation, a jihar Katsina dake arewacin Nigeriya, wadda uwargidan Gwamnan jihar Hajiya Fatima Ibrahim Shema ta kafa ta musamman domin taimaka ma yara masu fama da lalurar amosanin jini wato sickle cell a turance.

Filinmu na "In Ba Ku Ba gida" ya nemi wannan bakuwa tamu ta musamman domin ta fada ma masu sauraro ayyukan wannan kungiya tata, da fatan zaku kasance tare da mu.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China