in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yadda hankalin kasashen duniya ya karkata ga hare-haren da aka kai a Faransa
2015-11-19 09:29:39 cri

A ranar Jumma'a 13 ga watan Nuwamban shekarar 2015 da dare ne wasu 'yan bindiga masu da'awar jihadi suka kaddamar da hare-hare a sassa dabam-dabam na birnin Paris dake kasar Faransa, hare-haren da shugaban Faransa Francois Hollande ya bayyana da cewa, tsokana ce ta yaki. Kuma za su dauki dukkan matakan da suka dace domin kare hadin kan kasar.

Alkaluma na nuna cewa, mutane sama da 100 ne suka mutu kana wasu sama da 300 kuma suka jikkata. Wadannan hare-hare na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta Faransa ke kaddamar da hare-hare kan mayakan IS a kasar Syria.

Kungiyar IS dai ta dauki alhakin hare -haren da aka kai a birnin Paris, tana mai cewa, hare-haren martani ne ga yakin da sojojin Faransa ke yi da mayakan kungiyar.

Sai dai masu fashin baki na alakanta yadda harin ta'addanci da aka kai Faransa ya dauki hankalin duniya kan wasu dalilai. Na farko shi ne galibin kafafen yada labarai na duniya wato rediyo da talabijin da kuma kafofin sada zumunta na zamani kamar Facebook da Twitter da Google da dai sauransu dukkansu mallakar Turawa ne.

Na biyu shi ne alakar kasashen Turai da sauran kasashen duniya musamman a nahiyar Afirka wadda Turawa suka yi wa mulkin mallaka sun taimaka wajen kururuta batun hare-hare a nahiyar Turai.

Dalili na uku shi ne irin yadda shugabannin kasashen Turai suke nuna damuwarsu kan 'yan kasarsu sabanin yadda shugabannin kasashen Afirka ke nunawa kan nasu al'ummomin.

Tun bayan harin da aka kai wa Faransa jama'a a sassan kasashen Afirka suke ta mayar da martani tare da tafka muhawara, musamman a kafofin sadarwa na zamani kan yadda ake mayar da hankali kan wannan batu, Jama'a da dama na bayyana ra'ayinsu ne a kan yadda shugabannin kasashe da na kamfanoni na duniya suka rika mai da martani a kan hare-haren na birnin Paris, alhalin wasu makamantansu ko ma wadanda suka fi su muni sun faru ko dai a nahiyar Afirka ko wasu sassan duniya, amma ba a kula da su kamar haka ba.

Masu sharhi na ganin cewa, hanya guda ta magance matsalar ta'addaci ita ce, warware matsalar daga tushe. Sannan shugabanni su rika nuna kulawa da girmama abubuwan da ya shafi al'ummominsu a kowane lokaci. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China