in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron shugabannin Afirka da Indiya
2015-11-12 13:59:45 cri

A kwanakin baya ne kasar Indiya ta shirya wani taro da shugabannin kasashen nahiyar Afirka fiye da 50 a birnin Delhi, fadar mulkin kasar, taron da ya kasance irinsa na farko tsakanin sassan biyu.

Firaministan Indiya Nerandra Modi ya ce, an shirya taron ne da nufin bunkasa tattalin arziki, magance matsalar sauyin yanayi, makamashi maras gurbata muhalli, harkokin sufuri, tsarin noma na zamani, dabarun adana ruwa da kasashen nahiyar Afirka. Bugu da kari, Mr Modi ya bayyana cewa, Indiya za ta baiwa kasashen Afirka tallafin dala miliyan 600 don gudanar da ayyukan ci gaba

Masana na kallon taron a matsayin wani kokari da Indiya ke yi na zawarcin kasashen nahiyar Afirka da suka dade suna kyakkyawan dangantaka da kasar Sin domin gudanar da harkokin kasuwanci.

Bayanai na nuna cewa, kasuwancin da ke tsakanin Indiya da Afirka ya ninka zuwa dala biliyan 72 tun daga shekarar 2007, sai dai masana harkokin tattalin arziki na ganin cewa, wannan adadi bai taka kara ya karya ba.

'Yan Afirka da dama ne dai ke zuwa kasar ta Indiya don gudanar da harkokin karatu da neman jinya cikin rahusa, matakan da Indiya za ta kara amfani da su wajen kara bunkasa dangantakarta da kasashen na Afirka.

Sai dai masu fashin baki na cewa, da sauran tafiya kafin a iya tantance makomar wannan dangantaka tsakanin sassan biyu. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China