Bisa sakamakon wucin gadi da aka bayar, an ce, dan jam'iyyar kawacen hadin kan 'yan kasa ta Républican, kana shugaba mai ci na yanzu Alassane Ouattara ya samu kuri'un da yawansu ya kai miliyan 3.1, wadanda suka tashi zuwa kashi 83.66 cikin 100, wanda ya ba shi galaba kan abokin hamayyarsa Pascal Affi N'Guessan dan jam'iyyar adawa ta FPI.
An gudanar da zaben shugaban kasar a ranar 25 ga wata, kuma yawan masu kada kuri'u da suka yi rajista ya kai sama da miliyan 6.3, kuma yawan kuri'un da aka samu ya kai kashi 54.63 cikin 100.
Kwamintin tsarin mulki na Kwadivoire zai bayar da sakamakon zabe a gaban bainar jama'a har na tsawon kwanaki 8, idan babu rarrabuwar kawuna, kwamitin zai sanar da cewa, Ouattara ya sake cin zabe a hukunce.(Bako)