Ma'aikatar harkokin wajen Amurka a ranar Talatan nan ta soki hariin da kungiyar Boko Haram ta kai kwanan nan a Nigeriya. a cikin wata sanarwa da kakakin ma'aikatar John Kirby ya fitar, Amurka ta soki wannan munanan hare-hare, har na rashin imani a ranakun 23 da 24 na wannan wata.
Sanarwar ta ce, yin amfani da kananan yara, musamman 'yan mata wajen aiwatar da munanan hare-haren babban laifi ne, hakan na kara bayyana misalai na cewar, kungiyar ta Boko Haram a shirye take na ci gaba da gallaza wa fararen hula a arewacin kasar, da ma yankin tabkin Chadi.
A kalla mutane 27 ne aka tabbatar da mutuwarsu, wadansu 96 kuma suka jikkata a harin kunar bakin waken da aka kai a wani masallaci a garin Yola na jihar Adamawa a ranar Jumma'ar da ta gabata.
Wannan harin dai ya zo ne kasa da awanni 12 bayan wani da aka kai shi a wani masallacin a jihar Borno dake makwabtaka da Adamawa, wanda a nan kuma mutane 6 suka hallaka, wadansu 17 kuma suka jikkata.
Sanarwar ma'aikatar harkokin wajen ta Amurka ta mika juyayinta da ta'aziyya ga iyalai da masoyan wadanda wannan mummunan harin ya rutsa da su, wadanda yawancinsu fararen hula ne.(Fatimah)