in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fidda sakamakon rahoto game da jirgin saman Malaysia da ya fado a gabashin Ukraine
2015-10-29 16:19:48 cri

A ranar Talata 13 ga watan Oktoban shekarar 2015 ne, masu bincike a kasar Holland suka fidda rahoto game da musabbabin hadarin jirgin saman kasar Malaysia mai lamba MH17 wanda fado a ranar 17 ga watan Yulin shekarar 2014 a yankin gabashin kasar Ukraine, inda ta bayyana cewa, jirgin ya fado ne sakamakon harbo shi da aka yi da wata roka samfurin BUK kirar kasar Rasha,amma masu binciken ba su bayyana wanda ya harba rokar ba.

Kamfanin kera rokoki samfurin Buk mai suna Almaz-Antei na Rasha da kwamitin bincike kan hadarin jirgin sama na Ukraine suma sun fidda nasu rahotannin, inda suka zargi juna da haddasa hadarin jirgin saman na Malaysia.

Jirgin saman fasinjan na Malaysia mai lamba MH17 ya taso ne daga birnin Amsterdam a kan hanyarsa ta zuwa birnin Kuala Lumpur,dauke da mutane 298, ciki har da 'yan Holland kimanin 196 kuma dukkan fasinjojin sun mutu.

A cikin rahoton binciken, ba a ambaci wanda ya harba rokar ba, amma an nuna cewa, wurin da aka harba roka da ke gabashin kasar Ukraine yana karkashin ikon dakarun dake adawa da gwamnatin Ukraine ne .Binciken da ita ma Rasha ta yi, ya nuna cewa, sojojin gwamnatin Ukraine ne suka harba rokar.

Masu fashin baki na cewa, kamata ya yi tun farko hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta duniya ta hana zirga-zirgar jirage a yankin da ake tafka riciki,amma ba a yi hakan ba har lokacin da hadarin ya faru. Yanzu dai koma mene ne, masana na cewa, ko ba dade gaskiya za ta fito fili. (Ibrahim/Sanisu Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China