Shugaban kasar Tanzaniya Jakaya Kikwete, a ranar Asabar din nan, ya kaddamar da aikin sanya bututun sarrafa iskar gas mai tsawon kilomita 535 wanda ya lashe kudi dalar Amurka biliyan 1 da miliyan 225, wanda bankin Export-Import na kasar Sin ya samar da rancen kudaden aikin.
Aikin saka bututun, zai dinga tura iskar gas daga Mtwara dake kudancin Tanzaniya zuwa babban birnin kasar, Dar es Salaam, kuma kamfanin CPTDC na kasar Sin ne ya gudanar da aikin wanda aka fara shi a watan Yunin shekarar 2013.
Da yake jagorantar kaddamar da aikin, shugaba Kikwete na kasa, ya ce, aikin zai kawo karshen matsalar wutar lantarki da ya jima yana addabar kasar mafi karfin tattalin arziki a gabashin Afrika baya ga kasar Kenya.
Tanzaniya ta jima tana fama da matsalar wutar lantarki a sakamakon dogara da ta yi kacokan wajen amfani da samar da lantarki ta ruwa.
Babban daraktan sashen kula da albarkatun man fetur na kasar Dr James Mataragio ya ce, aikin sanya bututun, yana da karfin tura cubic 210 na iskar gas a kullum daga Msimbati dake Mtwara zuwa Kinyerezi dake birnin Dar es Salaam.(Ahmad Fagam)