in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wadansu jami'an kiwon lafiya a kasashen Afrika sun jinjina ma kyautar yabo a fannin likitanci da wata Basiniya ta samu
2015-10-07 14:51:00 cri
Jami'an kiwon lafiya a kasashen Afrika sun jinjina ma Tu Youyou bisa kyautar lambar yabo ta Nobel da ta samu a bangaren likitanci.

Alzouma Dari mukaddashin ministan kiwon lafiya na jamhuriyar Niger ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa sun ji dadin wannan labari cewar wata likita Basiniya ta samu wannan kyautar yabo a bangaren likitanci bisa ga aikin ta na magance cutar zazzabin cizon sauro.

Alzouma Dari wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake halartar taron ministocin kiown lafiya karo na biyu na kasashen Sin da Afrika a birnin Capetown na kasar Afrika ta kudu, ya ce kasar sa a koda yaushe ta na fama da cutar zazzabin cizon sauro a don haka zasu yi amfani da aikin ta da kuma ilimin ta wajen horas da jami'an kiwon lafiyarsu ta yadda za su shawo kan wannan cuta

Ita ma Ministar kiwon lafiya ta kasar Senegal Awe Marie Coll Seck ta bayyana farin cikin da jin dadinta kan yadda Madan Tu Youyou ta lashe wannan kyauta kuma ite ca wadda muke da fatan cewa, za ta ceto kasashen dake fama da zazzabin cizon sauro a Afrika.

Shima Aaron Motsoaledi ministan kiwon lafiya na kasar Afrika ta kudu cewa yayi sun yi matukar murna ganin cewa wannan lambar yabo ta je ga Basiniyar 'yar kimiyya , kuma kowa na son ganin bayan cutar zazzabin cizon sauro don haka suna taya ta murna da fatan alheri.

Dr Matshidiso Rebecca Moeti Daraktar kula da yankin Afirka na hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa gano maganin Artemisinin wani muhimmin cigaba ne don haka Madam Tu Youyou ta samu lambar ce saboda bajintar ta.

Madam Moete ta ce samar da wannan magani zai samar da sauyi a nahiyar Afrika matuka kuma za ta shiga wani mataki mai kyau na cimma muradan karni. Tana mai bayyana kasar Sin a matsayin sahihiyar abokiyar hadin gwiwwa a cigaban Afrika musamman kan yadda ta ke ci gaba ta tura ma'aikatan lafiya zuwa nahiyar

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China