in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar murnar cika shekaru 55 da samun 'yancin kan Najeriya
2015-10-11 12:13:35 cri

A ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1960 ne Najeriya, kasa mafi girma da yawan al'umma a nahiyar Afirka kana babbar abokiyar kasar Sin a fannin cinikayya, ta samu 'yancin kanta daga Turawan mulkin mallaka na kasar Burtaniya.

A irin wannan rana ce shugabannin a matakai daban-daban na kasar kan shirya shagulgula don murnar wannan rana inda ake bitar irin nasarorin da aka cimma ya zuwa wannan lokaci da kuma sassan da ke bukatar kara ingantawa.

Bisa al'ada shugabanni kan gabatar da jawabai ta gidajen rediyo da talabijin inda suke tilawar zangon da aka cimma da kuma inda ake fatan dorawa a kai.

Masana na cewa, duk da abin da ba za a rasa ba,zangon da Najeriya ta cimma cikin shekaru 55 da suka gabata, abin a yaba ne, ganin yadda kasar ta kasance a hade duk da bambance-bambancen addini, kabila da na siyasa.

Sai dai masu sharhi na ganin cewa, sabbin shugabannin da talakawa suka zaba a yayin zabukan da suka gabata a kasar, yanzu kasar ta doshi samun makoma mai haske. Da fatan 'yan kasa za su kasance masu kishin kasa da baiwa shugabannin hadin kan da ya dace a kokarin da su ke na samar da kayayyakin more rayuwa,tsaro,yaki da talauci da samar da aikin yi ga matasa, uwa uba da mai do da darajar kasar a idon a duniya. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China