in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu za ta shirya dandalin Sin da Afrika cikin hadin gwiwa kan kiwon lafiya
2015-09-29 11:19:38 cri
Kasar Afrika ta Kudu za ta shirya dandalin ministocin Sin da Afrika karo na biyu kan cigaban kiwon lafiya.

Wannan dandali zai gudana daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Oktoba a birnin Cape Town, bisa taken "bunkasa ingancin ayyukan kiwon lafiya a Afrika da kuma kyautata dangantakar hadin kai tsakanin Sin da Afrika game da kiwon lafiyar jama'a bayan annobar Ebola", in ji wani jami'i a fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jeff Radebe.

Wannan tsari ya biyo daga dandalin tattaunwar hadin kai tsakanin Sin da Afrika, dake daukar kiwon lafiya a matsayin wani muhimmin mataki na dangantakar Sin da Afrika, in ji mista Radede.

Dandalin farko na Sin da Afrika kan cigaban kiwon lafiya ya gudana a cikin watan Augustan shekarar 2013 a birnin Beijing.

Dangantakar kiwon lafiya tsakanin Sin da Afrika ta samu karfafuwa a lokacin barkewar annobar cutar Ebola a wasu kasashen yammacin Afrika.

Baya bayan nan kasar Sin ta samar da taimakon kayayyaki da kudade domin taimaka wa wajen kawar da yaduwar cutar Ebola a yankin.

Wannan dandalin kiwon lafiya ya zo watanni biyu kafin babban taro na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afrika (FOCAC), da Afrika ta Kudu za ta shugabanta cikin hadin gwiwa, wanda kuma aka tsaida shiryawa a ranakun 4 da 5 ga watan Disamba a birnin Johannesburg. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China