A kalla mutane biyar suka mutu, wanda ya hada da dan sanda guda, a yayin da aka kai wani harin kunar bakin wake a wata tashar tsaro dake kunshe da jami'an tsaro na 'yan sanda, garda sarki da kuma sojoji, a ranar Lahadi da safe a yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru, a cewar wasu majiyoyin soja.
Harin da ake ganin akwai hannun kungiyar Boko Haram, ya faru ne a Mora, wani yankin dake iyaka da Najeriya, mai tazarar kilomita 80 daga Maroua, muhimmin birnin dake kuriyar arewacin kasar Kamaru. (Maman Ada)