in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimmancin ziyarar da shugaba Xi zai kai Amurka ga sassan biyu
2015-09-27 10:57:01 cri

Daga ranakun 22 zuwa 25 ga watan Satumban shekarar 2015 ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya kai ziyara kasar Amurka, ziyarar da ake fatan za ta kasance wata dama ta fadada hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Wannan ita ce ziyarar aiki ta farko da Xi Jinping ya kai Amurka a matsayin shugaban kasar Sin, lamarin da masana ke ganin cewa, wata muhimmiyar dama ce ta bunkasa zaman lafiya da samun moriyar juna tsakanin sassan biyu.

Bugu da kari, ana sa ran shugabannin kasashen biyu za su cimma yarjejeniya a fannonin da suka shafi harkokin kudi, cinikayya da makamashi, batun sauyin yanayi, kimiya da fasahar kere-kere da sauransu.

Duk da cewa, ziyarar za ta taimaka wajen bunkasa dangantakar manyan kasashen biyu, masana na ganin cewa, zai yi wahala sassan biyu su warware wasu daga cikin manyan bambance-bambancen da ke tsakaninsu dangane da batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

A yayin wannan ziyara ce kuma, shugaba Xi zai halarci bukukuwan cika shekaru 70 da kafuwar MDD tare da gabatar da muhimmin jawabi, inda ake sa ran zai bayyana akidar kasar Sin na tabbatar da zaman lafiya a duniya. Shugaban Xi zai kuma halarci taron shugabannin kasashe masu tasowa, kungiyoyin mata da 'yan kasuwa da masu masana'antu da sauransu.

Masu fashin baki na cewa, ziyarar za ta taimaka wajen rage zaman tankiya da bahaguwar fahimta tsakanin sassan biyu kan wasu muhimman batutuwa kamar, satar bayanan intanet, kare hakkin bil-Adam, tsaron nukiliya da makamantansu. Inda ake fatan karkaka ga batun cinikayya, amincewa da mutunta da juna da sauran matakan inganta rayuwar bil-adam da uwa uba samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. (Ibrahim/Sanusi chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China