in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matsalar bakin haure a nahiyar Turai
2015-09-17 19:50:55 cri

Duk da matakan da hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Turai ta EU ta bullo da shi na rarraba baki 'yan ci-rani da ke shigowa nahiyar tsakanin kasashe mambobin kungiyar 28, har yanzu tula ba ta rabu da kalaye ba.

Hukumar EU ta ce, ta dauki wannan mataki ne don ganin an kawo karshen halakar da 'yan ci-ranin ke yi a tekun Bahar-Rum a kokarin da su ke yi na neman shiga Turai ko ta halin kaka.

Wasu kasashe mambobin kungiyar sun ce su kam ba za su lamunci wannan tsarin ba, yayin da ita kuma kasar Jamus ta yi maraba da shi. Karkashin sabon tsarin kungiyar EU, duk kasar da ta amince ta tsugunar da bakin da ke shiga kasashen na Turai, za ta samu tallafin kungiyar.

Hukumar zartaswar kungiyar EU ta tsara shirin ne bisa yawan al'ummar kasashen da kuma yawan GDPn da ta kowace kasa ke samu, wato kasar da ta fi yawan mutane da GDP yana nuna cewa, tana da karfin karbar karin 'yan gudun hijira. Wannan tsari ya haifar da sabanin ra'ayi tsakanin kasashe mambobin kungiyar.

Bakin haure dai na barin kasashensu na asali ne sakamakon tashin hankali ko matsalar tattalin arziki ko wasu nau'o'in bala'u daga indallahi da nufin shiga Turai ko za su fita daga matsalar da ta gallabe su.

Bayanai na nuna cewa, mutane da dama ne ke rasa rayukansu a teku a kowace shekara a kokarin shiga Turai ta kwale-kwale marasa inganci.

Alkaluman baya-bayan nan sun bayyana cewa, sama da bakin haure 80,000 ne suka yi kokarin shiga Turai a wannan shekara kadai.

Masu fashin baki na ganin cewa, hanya daya tilo ta magance wannan matsala ta 'yan ci-rani da ke kokarin shiga Turai ita ce, gwamnatocin kasashen da bakin hauren ke fitowa su raya tattalin arziki da tabbatar da zaman lafiya a kasashensu da inganta rayuwar al'ummominsu kamar yadda ake fata. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China