A yayin shawarwarin, kasar Sin ta jaddada cewa, idan wata kasa ta zabi hanyar da take bi, bisa halin da kasar take ciki da kuma bukatun jama'arta, bai kamata kasashen ketare su tsoma baki cikin harkokin gidanta ba. Ya kamata kasar Sin da kasar Amurka su gani yanayin hakkin dan Adam na kasashen yadda ya kamata bisa ka'idojin nuna mutuntawa da adalci, su kuma warware sabanin dake tsakaninsu kan harkokin dake shafar hakkin dan Adam ta hanyoyin yin shawarwari da hadin gwiwa, ta yadda za a iya amfanawa kasashen biyu wajen gina wata sabuwar dangantaka ta manyan kasashe.
Bugu da kari, kasar Sin ta gabatar da wasu tambayoyi ga kasar Amurka dangane da harkokin wariyar launin fata, yin amfani da karfin tuwo da bai dace ba da 'yan sandan kasar suke yi, da kuma leken asirin manyan jami'an ketare da dai sauran harkokin keta hakkin dan Adam da kasar Amurka ta aikata.
Kana bayan shawarwarin, wakilan kasar Sin sun yi taron kara wa juna sani tare da mataimakan 'yan majalisar dokokin kasar Amurka da wasu masanan da abin ya shafa, haka kuma, sun kai ziyara a wani yari dake birnin Montgomery na jihar Maryland ta Amurka. (Maryam)