Ya zuwa karfe 12 na ranar yau, fashewar ta haddasa rasuwar mutane guda 44, ciki hada da 'yan aikin kwana-kwana guda 12, kana wasu mutane 520 suna karbar jinya a asibiti, 66 daga cikinsu suna ji rauni mai tsanani.
Fashewar ta auku ne a wani dakin da ake ajiye sinadarai masu matukar hadari, kuma rahotanni sun nuna cewa, gine-gine, wuraren ajiye motoci da wasu wuraren da ke kusa da wurin fashewa sun kama da wuta sakamakon fashewar.
Har zuwa yau da safe ana iya ganin wuta na ci yayin da hayaki ya turnuke wurin, yayin da a wasu lokutan gilasai ke fadowa daga sama , haka kuma, fashewar ta lalata kamfanoni guda shida dake kusa da wurin. Ana kuma kiyasin cewa,kashi daya bisa shida na motoci dubu shida da ake wani wurin ajiye motoci sun kone. (Maryam)