in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hajiya Ladi Mairo Shambo
2015-09-08 17:08:22 cri

Yau shirin In Ba Ku Ba Gida yana farin cikin gayyato wata bakuwa mai suna Hajiya Ladi Mairo Shambo, wadda ta kasance tsohuwar malamar makaranta, ta dade tana ba da horo ga matan karkara a fannin sana'o'in hannu kamar yadda ake hada man kade, alaiyadi, sabulun salo, sabulun wanki da dai sauransu, har ma da kayan amfani ta fannin girki kamar su yaji da kayan kamshi.

A tattaunawarta da wakiliyarmu Fatimah Jibril, Hajiya Ladi Mairo Shambo ta bayyana tarihin rayuwarta, da kuma yadda take kokarin inganta rayuwar mata. A ganinta in mata ba su samu karfi a zukatansu ba wato zuciya ya mutu to ba za su iya tashi tsaye da kafafunsu ba, to, babu wanda zai iya taimaka musu wajen yakar talauci da samun wadata ba. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China