in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Obama a nahiyar Afirka
2015-08-06 15:52:53 cri

A ranar Asabar 25 ga watan Yulin wannan shekara ce shugaban kasar Amurka Barack Obama ya halarci taron kolin harkokin masana'antu na kasa da kasa karo na shida da aka yi a birnin Nairobi, fadar mulkin kasar Kenya inda ya bayyana cewa, Amurka na nuna kyakkyawan fata ga bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afrika.

Shugaba Obama ya ce, a matsayin daya daga cikin nahiyoyin da suke samun saurin bunkasuwa, Afrika tana iya zama muhimmin ginshiki wajen samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya a nan gaba. Kuma gwamnatin Amurka za ta hada kai da bankuna, asusu da kungiyoyin kula da jin kai don tattara kudi har dala biliyan 1 a kokarin tallafa wa ayyukan kafa kamfanoni a duniya, musamman ma ga mata da matasa a Afrika.

Sai dai kwararru sun yi gargadin cewa, ziyarar da shugaban Amurka ya kai kasar Kenya ba za ta magance tarin kalubalolin da kasar da ma nahiyar ke fuskanta ba.

Masana kan harkokin diflomasiya a jami'ar Nairobi da ke kasar ta Kenya sun kuma gargadi takwarorinsa da kada su yi tsammanin marabbuka daga gwamnatin Amurka. Domin ba kasafai talaka yake amfana daga irin wadannan dangantaka tsakanin kasa da kasa ba.

Masu fashin baki na bayyana cewa, kasar Kenya da sauran yankunan da ke kudu da hamadar Sahara sun amfana matuka daga huldar da ke tsakaninsu da kasar Sin kamar bangaren sufuri, sadarwa, kayayyakin more rayuwa, makamashi, harkar lafiya, ilimi, kasuwanci da kuma al'adu, baya ga gajiyar tallafin kudi da fasahohi ba tare da wasu sharudda ba.

A jawabin da shugaba Obama ya yi a zauren kungiyar AU da ke Addis Ababa na Habasha, ya kalubalanci shugabannin Afirka da su guji dauwama a kan karagar mulki, sannan su yaki cin hanci, kyauta batun kare hakkin bil-Adama da mulki na gari, 'yanci ga mata da inganta rayuwar al'umma da samar da ayyukan yi ga matasa.

Sai dai masana na cewa, har yanzu Amurkan ta gaza samar da wani muhimmin taimako don magance manyan kalubalolin da nahiyar Afirkan ke fuskanta. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China