Ya kuma samu tabo a filin saukar jigaren sama na kasa da kasa dake Nairobi daga takwaransa na kasar Kenya Uhuru Kenyatta, tare da sauran mambobin gwamnatin Kenya.
'Yan sanda sun kiyaye tsaron filin jirgin saman da manyan makamai. Domin kare tsaron lafiyar shugaba Obama, 'yan sanda dubu goma aka jibge a muhimman wuraren kasar.
Mun dauki karin matakai dalilin yawaitar hare haren kungiyar Al-Shebaab dake fitowa daga kasar Somaliya da za su iya kawo hatsaniya ga wannan ziayara, in ji wani jami'in 'yan sandan Kenya.
Manyan jami'an tsaron kasar Amurka sun isa birnin Nairobi 'yan makwanni kadan kafin zuwan shugaba Barack Obama.
A birnin Nairobi, mista Obama zai halarci wani dandalin kasa da kasa na masu masana'antu (GES), shirin da Amurka ta kirkiro da kuma ke gudana a karon farko a wata kasar da ke kudu da hamadar Sahara. (Maman Ada)