Shugaban tawagar wakilan kasashen Afrika dake nan kasar Sin, kuma jakadan kasar Madagscar dake nan kasar, mista Victor Sikonina ya gabatar da jawabi a yayin bikin, inda ya nuna yabo sosai kan hadin gwiwar irin na samun moriyar juna a tsakanin Afirka da Sin a cikin shekaru 50 da suka wuce, sa'an nan ya nuna yabo kan muhimmiyar rawar da Sin ke takawa wajen canja yanayin da Afirka ke ciki.
Kasar Zimbabwe ce ke shugabantar kungiyar AU a wannan karo, jakadan kasar dake nan kasar Sin mista Paul Chikawa yayi jawabi cewa, shekarar da muke ciki shekara ce ta cikon shekaru 15 da aka kafa dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afirka, kuma ita ce ta cika shekaru 50 da Sin ta turo tawagar likitanci ta farko zuwa Afirka, haka kuma ya nuna godiya ga kokarin da Sin ke yi na taimakawa Afirka wajen tabbatar da ci gaba daga dukkan fannoni.
A nasa bangaren, mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin mista Zhang Qingli a cikin jawabinsa a madadin gwamnati da jama'ar kasar Sin ya taya murnar bikin ga gwamnatoci da jama'ar kasashen Afirka, inda kuma ya nuna yabo sosai kan nasarorin da kasashen Afirka suka samu ta hanyar hadin kai, ya ce, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan marawa kasashen Afirka baya a kokarinsu na neman ci gaba bisa hadin kan juna da dunkulewar kasashen Afirka bai daya, ko da yaushe tana goyon bayan kasashen Afrika wajen raya kasashensu. Zhang ya kara da cewa, kasar Sin za ta kara yin hadin kai tare da kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka, tare da taimaka wa kasashen Afrika wajen kara wakilcinsu da kuma ikon bayyana ra'ayinsu a harkokin duniya. (Bilkisu)