Madam Li Bin ta ce, ba za a iya raba wannan aiki da shirin yin gyare-gyare da raya harkokin kiwon lafiya ba. Yanzu, Sin na karfafa shirin yin gyare-gyare game da tsarin kiwon lafiya, don bullo da wani tsarin ba da hidima, da tsarin ba da inshora, da tsarin samar da magunguna, har ma da tsarin sa ido, don kafa wani tsarin da zai shafi duk kan jama'a.
A sa'i daya kuma, tsarin kiwon lafiya yana bukatar hadin gwiwar kasashen duniya. Bayan da aka karfafa hadin gwiwar kasashen duniya,sai kuma aka fuskanci matsalar cututtuka da ke yaduwa tsakanin kasashen daban-daban, lamarin da ya kawo babbar illa ga tsarin kiwon lafiya, domin ba wata kasa da za ta warware irin wannan matsala ita kadan ta.
Li Bin ta ce, yayin da ake yaki da cutar Ebola, gwamnatin Sin ta ba da agajin da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 120 ga kasashen yammacin Afrika, kuma ta tura ma'aikatan kiwon lafiya sama da 1200 don yaki da cutar.
Sannan bayan da aka samu girgizar kasa mai karfin maki 8.1da ta abkawa kasar Nepal, gwamnatin Sin ta tura kungiyoyi masu aikin jinya guda 4 don ceton mutanen da bala'in ya shafa.(Bako)