in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Halin da yaran da ke gudun hijira a Tarayyar Najeriya ke ciki
2015-05-05 10:52:27 cri


Ranar 26 ga watan Afrilu, rana ce ta yara ta duniya, wato "World Children's Day", wanda aka kaddamar da ita a shekara ta 1986. Ana tunawa da wannan rana ce a sakamakon wata wasika da wata yarinya mai suna Funda Karagozler mai shekaru 9 da haihuwa a wancan lokaci daga kasar Turkiya ta rubuta wa yaran kasashen duniya, inda ta bayyana fatanta na zaman daidai wa daida a cikin unguwanninsu, da samun wata duniya mai zaman lafiya. Kamar yadda ta ce, "Ko da yake mu yara ne, amma muna son kyautata wannan duniya.". Daga bisani kuma, an mika wannan wasika zuwa ga asusun kula da yara na MDD da kuma wakilan mambobin majalisar, wanda ya samu martani sosai daga wajensu. Sabo da haka, an mai da ranar Lahadi ta hudu ta ko wane watan Afrilu a matsayin ranar yara ta duniya, inda a kan gayyaci wakilan yara daga kasashe daban-daban zuwa babbar hedkwatar MDD da ke NewYork domin sauraron burinsu da kuma gudummawar da suka bayar ga unguwannin da suke zaune.

Yayin da muke ambaton yara a wannan rana, a ganina, abin da ya fi jawo hankalina da ma masu sauraronmu shi ne batun 'yan gudun hijira yara da ke Tarayyar Najeriya, wadanda suka rasa gidajensu sakamakon harin ta'addanci da kuma mummuman yanayin tsaro. Don haka yau shirin In Ba Ku Ba Gida ya gayyaci Hajiya Hadiza Sani Kangiwa, kwamishiniyar dake jagorantar hukumar kula da harkokin 'yan gudun-hijira, da bakin haure, gami da mutanen da suka rasa matsugunansu a Najeriya, inda ta yi bayani kan batun yaran da ke gudun hijira da kuma matakan da ake sauka don warware wannan matsala. Masu sauraro, muna fatan kuna kusa da akwatunan rediyonku domin sauraron wannan hira da wakilinmu Murtala ya yi da Hajiya Hadiza Sani Kangiwa.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China