in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawa 4 mata sun samu gurbi a gasar Tenis ta Faransa
2015-04-23 09:38:51 cri
Shahararriyar 'yar wasan Tenis ta kasar Sin Peng Shuai, da wasu 'yan wasa uku sun samu guri kai tsaye, na halartar gasar kwallon Tanis ta 114 da za a buga a Faransa, daga ranar 24 ga watan Mayu zuwa 8 ga watan Yuni mai zuwa.

Bisa tsarin gasar wadda za ta kunshi ajin mata da na maza, akwai 'yan wasa 128, da suka hada da 'yan wasan alfarma 8 wadanda nan gaba za a bayyana sunayen su.

Cikin 'yan wasa mata 108 da aka zayyana sunayen su, akwai Peng Shuai da aka ayyana a matsayi na 21, da Zheng Saisai ta 74, da Zhang Shuai ta 81, da kuma Wang Qiang wadda ke matsayi na 96 bisa jerin kwarewar 'yan wasan Tanis na duniya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China