in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shang Yaoqian, yarinya ce da ta kware a fannin rawar ballet
2015-06-09 15:43:23 cri

Kasar Burtaniya Aljannar duniya ce ga masu sha'awar fasahohi, duba da yadda ta ke da yawan gidajen aijiye kayayyakin tarihi, da wasannin kwaikwayo na kide-kide. Ga wadanda ke fatan mayar da fasaha a matsayin ayyukansu na rayuwa, Burtaniya ta kasance wuri na gwaji, inda akan zabi fitattu daga cikinsu, tare kuma da yin watsi da marasa kwarewa.

A kwanan baya, wata yarinya mai shekaru 22 a duniya, ta bayyana mana yadda take kokarin tabbatar da burinta na zama tauraruwa a rawar ballet, a kasar ta Burtaniya. A cikin wannan shiri na mu, za mu more labarinta, tare da ku masu sauraronmu.

Lambar yabo ta fitattun matasa ta Mu-Lan, wadda aka bayar a kasar Burtaniya a shekarar 2014, ta zamo babbar kyauta ga Shang Yaoqian, kana wani abu mai ban mamaki gare ta.

"Wata rana muna kokarin gwada kwaikwayo ne, a lokacin wani abokin aiki na ya buga min waya, cewar akwai wani labari mai kyau, "kin samu lambar yabo ta Mu-Lan". A gaskiya ban san me ya faru a lokacin ba, sai na ba da amsa cewa, 'OK' ."

An kaddamar da lambar yabo ta Mu-Lan ne a shekarar 2009, da nufin yabawa Sinawa mata dake kasashen ketare. Mambobin hukumar kimanta lambar yabon shun hada da uwar gidan tsohon firaministan kasar Burtaniya Tony Blair, da Li Meichan, da shahararriyar babbar akanta ta kasar, kuma 'yar asalin kasar Sin, wadda tana daya daga cikin wadanda suka kafa wannan lambar yabo ta Mu-Lan, da dai sauransu.

Samun lambar yabo ba wani abin mamaki ne ga Shang Yaoqian. A hakika dai, a shekarun baya saboda samun lambar yabo ta matsayi na uku da ta yi a gasar rawa ta ballet ta matasan Amurka, ta samu damar koyon rawar ballet a kasar Burtaniya. Bisa maki mai kyau da ta samu a yayin wancan gasar, kungiyoyin rawar ballet guda hudu suka bayyana fatan samar mata kudin bonas, ciki kuwa guda biyu sun fito ne daga manyan kungiyoyin rawar ballet guda shida na duniya, wato kungiyar rawar ballet ta Amurka, da kungiyar rawar ballet ta sarautar Burtaniya. A karshe dai, Shang Yaoqian ta zabi ta baya.

A shekarar 2011, Shang Yaoqian ta bar makarantar sakandare, ta kwalejin koyon fasahohin raye-raye da ta dade ta na karatu har shekaru 7 a wurin, ita kuma da kanta ta tafi birnin London duk da nisan sa, don kara karatunta.

Amma, kafin hakan, muhimmiyar hanya da ta bi wajen fahimtar wasannin kwaikwayon rawar ballet na yammacin duniya, ita ce kallon faifan kwamputa.

"Na yi tunanin cewa, akwai wanda zai kawo mana wasu faye-fayen kamputa, sai mu yi ta zaba, mu yi ta zaba, har mun samu wadanda muke bukata. Gaskiya wannan ne daya daga cikin hanyoyi kadan da muka bi wajen fahimtar yadda kungiyoyin rawar ballet, na kasashen ketare suke a wancan lokacin."

Sarauniyar ballet ta kasar Faransa, Sylvie Guillem abun-koyi ce ga Shang Yaoqian.

"A bara, a karon farko na kalli rawar da ta yi a filin wasannin kwaikwayo. Ta yi rawa kan kusan dukkan wasannin kwaikwayon ballet, har ma an tsara mata wasu sabbin wasannin kwaikwayo na musamman. A ganina, ita wata abar al'ajabi ce."

Amma, ba cikin sauki ba ta zama wata al'ajabi. A yayin da take karatu a birnin London, ba ya ga kokarin gwada kawa, da matsaloli da ta fuskanta a fannonin zaman rayuwa, a daya hannun ta bukaci hadin kai, da yin takara da masu rawar ballet daga kasashe daban daban. Game da dalilin da ya sa ta zabi irin wannan rawa ta ballet kuwa, wadda ke bukatar horo mai tsanani da karfin jiki sosai, Yao Shangqian ta gaya mana cewa, babu wata dabara, saboda ta kasance mai sha'awar yin rawa tun daga yarintar ta. Kuma tun da ta zabi sauran irin raye-raye ma ta na bukatar kokari sosai. Ko da yake ta zubar da gumi da hawaye da yawa, amma, yanzu ta samu sakamako mai kyau. Ta ce, tana jin dadi a wancan lokaci, wato ta tsaya a cibiyar dandalin wasan kwakwayo, kuma dukkan masu kallo sun zura mata ido.

"A cikin mintoci 10 zuwa 20, dukkan mutanen dake kallo idon su na kan ta. A wani irin yanayi mai kama da dabo.

A shekarar 2013, Shang Yaoqian ta gama karatu a kungiyar rawar ballet ta sarautar Burtaniya, a wannan shekara ne kuma, ta zama 'yar wasa ta kungiyar rawar ballet ta Birmingham ta sarautar Burtaniya. Ya zuwa yanzu ta riga ta zama babbar 'yar wasa a cikin wasu shahararrun wasannin kwaikwayo na duniya.

Bayan kallon yadda Shang Yaoqian ke yi cikin wasan kwaiwayo na "Beauty and the Beast", mai kimanta wasannin kwaikwayon rawar ballet na kasar Burtaniya, Kerry Assinder ya rubuta cewa, "rawar da Shang Yaoqian ta yi, ta yi matukar jawo hankalin masu kallon wasan, ana jin nishadi da annashuwa yayin da ake kallon wasanta."(Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China