in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matakan magance ayyukan ta'addaci a yankin tafkin Chadi
2015-04-12 16:04:43 cri

A kwanakin baya ne ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius, ya je birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar a wani rangadin yaki da ta'addanci,inda ya yaba da matakin da Nijar ta dauka wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Kafin ya isa babban birnin Nijar, minista Laurent Fabius sai da ya yada zango a birnin N'Djamena na kasar Chadi da kuma birnin Yaounde na kasar Kamaru, a wani rangadin da ya shafi yaki da ayyukan kungiyar Boko Haram musammun ma a wadannan kasashe uku dake makwabtaka da Najeriya.

Ayyukan na Boko Haram sun tilastawa kasashen Nijar, Chadi da Kamaru, daukar matakan hadin gwiwa wanda masu fashin baki ke cewa,kamata ya yi gamayyar kasa da kasa ta yaba da shi.

Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya bayyana kudurin kasarsa na samun nasara kan mayakan na Boko Haram.

Yankunan Bosso da Diffa da ke Jamhuriyar Nijar sun fuskanci jerin hare- hare daga mayakan kungiyar wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 15 a bangaren jami'an tsaro na FDS, a yayin da aka kashe mayakan Boko Haram kusan 280 kana aka cafke wasu kimanin 160.

Baya ga ziyarar Fabius, suma shugabannin kasashen Togo da Benin sun kai ziyara kasar ta Nijar don nuna goyon bayansu ga gwamnati da al'ummar Nijar kan matakan da suka dauka na yaki da ta'addanci.

Wadannan ziyarce-ziyarce na zuwa ne bayan da kasashen da ke tafkin Chadi suka kafa rundunar hadin gwiwa don yaki da matsalar mayakan Boko Haram da ta gallabi yankin.

Masana na ganin cewa,wannan mataki da kasashen da ke yankin tafkin Chadi suka dauka da kuma yunkurin kasashen ketare kamar kasar Faransa, zai taimaka wajen kawo karshen ayyukan ta'addanci da suka yi sanadiyar rayuka da dukiyoyin jama'a a yankin da ma nahiyar Afirka baki daya.

Sai dai masu sharhi na ganin cewa,jami'in na Faransa ya kai rangadin ne da nufin ganin an kare kaddarorin Faransa da ke kasar ta Jamhuriyar Nijar ba wai taimakawa kasar ta magance matsalar tsaron da ke fuskanta ba.

Don haka, suka ce kamata ya yi a bar 'yan kasar da makwabtansu su magance wannan matsala da kansu maimakon tsoma baki daga kasashen ketare. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China