in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron shekara-shekara na NPC
2015-03-15 10:11:12 cri

A yau ranar 15 ga wata da safe, aka rufe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, NPC wanda aka kwashe kwanaki 10 ana yinsa a nan birnin Beijing.

Mr. Zhang Dejiang, shugaban majalisar NPC ne ya shugabanci bikin rufe wannan taron.

A yayin taron, wakilan jama'a sun tattauna tare kuma da zartas da jerin takardu, ciki har da rahoton aiki na gwamnati, da rahoton bunkasa tattalin arziki da zaman rayuwar al'ummar Sin da shirin kebe kasafin kudi.

Sannan kuma sun amince da rahotannin da kotun kolin kasar Sin da hukumar koli ta bincike ta kasar suka gabatar game da ayyukan da suka yi a shekarar 2014. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China