150309-Ranar-mata-ta-duniya-Bilkisu.m4a
|
Mata na taka muhimmiyar rawa a cikin gida da kuma al'umma, kamar yadda taken shirinmu ya nuna,wato mata in ba ku ba gida. Saboda muhimmancin mata, ya sa aka kebe wata rana don mata, wato ranar takwas ga watan Maris ta ko wace shekara. A bana, ranar Lahadin da ta gabata, rana ce ta mata ta duniya, don haka, yau mu tsara wannan shirin musamman don wannan rana ta mata ta duniya.