Wani babban jami'in diplomasiyyar kasar Rasha ya bayyana cewa, hukumomin Moscow a shirye suke wajen ci gaba da aiki tare da hukumomin Washington kan ajiye makaman nukiliya a duk lokacin da suka samu karin haske daga kasar Amurka dake zargin Rasha da take sabawa yarjejeniya a kan wannan batu.
Mun sha bayyana wa abokanmu na Amurka cewa, a shirye muke mu ci gaba da tattaunawa, in ji mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Serguei Ryabkov, a wani labarin da kamfanin dillancin labarai na RIA Novosti ya rawaito.
Amma kuma jami'in diplomasiyyan ya jaddada cewa, hukumomin Moscow na bukatar da farko sanin dalilin da ya sa Amurka ke zargin Rasha da take sabawa yarjejeniyar da shafi karfin nukiliya na matsakaicin zango (FNI). Yarjejeniyar dai, an rattaba hannu kan ta a shekarar 1987 da zummar kawar da manyan makamai da makaman nukiliya. (Maman Ada)