
Firaministan kasar ta Sin ya gudanar da ziyarar tasa ne gabanin shiga sabuwar shekarar gargajiyar Sinawa, inda ya yi amfani da wannan dama, wajen gabatar da sakon fatan alheri na sabuwar shekarar ga daukacin al'ummar kasar.
Kaza lika Mr. Li ya bukaci mahukunta da su kara kwazo, wajen bunkasa harkokin kula da lafiyar al'umma, da na kare muhallin halittu, da harkar samar da ababen more rayuwa, duba da muhimmancin da hakan ke da shi ga rayuwar mazauna karkara.




